Abun Da Yakamata Kusani Akan PayPal AccountPayPal Kamfani ne mallakin kasar Amurka wanda ake amfani dashi wajen turawa da amsar dollar a tsakanin nahiyoyi ko kuma kasashen duniya.

Yan kasuwa masu harkalla da kasashen duniya, da ma'aikata masu aikin wucin gadi ko kuma aikin yi a biya irin su freelancing, affiliate marketing da sauransu sune sukafi amfani da PayPal domin samun sauki wajen turawa ko kuma amsar dollar.

PayPal yina aiki a ko wacce Nahiya amma sai dai kuma akwai kasashen da aka haramta ma aiki dashi musamman wajen amsar kudi. Nigeria tana daya daga cikin kasashen da aka haramta ma amsar kudi daga PayPal saboda yawan yan damfara da Nigeria ke dasu. Amma kuma mutumin dake Nigeria, yina iya tura kudi domin siyan wani abu ko kuma biyan kudin aiki idan anyi masa.

A PayPal akwai account kala biyu, personal account da kuma Business account. Idan mutum zai buɗe PayPal, a shawarce Yafi kyau ya bude Business account saboda shi wannan account ɗin yina da alfanu masu yawa musamman ma ga yan Nigeria da kuma kasashen da aka hana amsar kudi ta PAYPAL. Saboda yina basu damar da zasu iya biya kuma su amsa kudi.

Bude PayPal abu ne mai matukar sauki sosai musamman idan ya zama personal account zaka bude. Wanda zai bude Business account yina bukatar ilimi akan yadda akeyi sosai ko kuma yaje ya samu wanda ya iya ya bude masa, saboda gudun matsala.

Wanda ke da shirin bude PayPal account yina bukatar abubuwa kamar haka:

1- E-mail address
2- NIN Number
3- Phone Number
4- ATM card: ba ko wanne irin ATM card suke amsa ba, mai budewa idan yaje budewa zai ga wadanda suke bukata.
5- Google Invoice: ita wannan lamba ce ta kasar waje, amma amfani da ita wajen bude personal PayPal account ba dole bane sai dai idan Business account mutum zai buɗe.

A takaice wannan shine bayani akan PAYPAL account.

Post a Comment

Previous Post Next Post