Bayani akan Google AdSense (1)
Bayani akan Google AdSense (1)

Google AdSense wani sashi ne na kamfanin Google wanda aka kirkiro shi a 2003 kuma aka dawwamar dashi a shekarar 2005 bayan kamfanin sun tabbatar da cewa kaso mafi rinjaye na ribar da suke samu, yina zuwa ne daga ɓangaren AdSense.

Dalilin ƙirƙirar Google AdSense, shine a Bama yan kasuwa damar tallata hajojin su a manyan shafukan na yanar gizo dake ko ina a faɗin duniya. Haka zalika, an kirkireshi ne domin a samar ma Bloggers da Vloggers hanyar kudin shiga. 

Yan kasuwa masu buƙatar tallata kayansu, suna tallatawa ne ta hanyar yin Register sashin Google AdWords sannan su biya kudi domin a tallata masu kayansu dai-dai da yadda suke so. Su kuma Bloggers da Vloggers suna amsar wannan tallar ne a hannun kamfanin Google ta sashen Google AdSense. 

Google suna fara bama mutum talla ne ta hanyar Google AdSense Idan shafin shi ya cika wasu ƙa'idoji nasu. Waɗannan ƙa'idojin sun haɗa da;

1- Mutum ya ƙirƙirar shafin mai kyau wanda yake user friendly

2- Mutum ya samu official domain kamar irinsu .com .ng ko .com.ng da sauran su, Google ba zasu baka talla ba da .blogspot.com ko . wordpress.com ko .zamani.site

 3- Za'a fara baka talla ne idan ka samu a ƙalla mutum 50 suna ziyartar shafin ka a ko wacce rana.

4- Google ba zasu fara baka talla ba idan ya zama content ɗinka kana kwafo shine daga wani waje (suna da tsauri sosai akan Copyright).

5- Kafin a fara baka talla a shafin ka, anan bautar ka saka rubutu masu jan hankali a ƙalla guda 30 ko 40.

6- Idan Youtube channel kake dashi, kafin ayi monetizing ɗinka a fara baka talla sai ka samu subscribers 1000 a channel dinka tare da kuma 3000hrs of views a channel ɗinka. 

Mai buƙatar yin Register da Google AdSense yina iya ziyartar shafin su na www.adsence.com 

Google AdSense dai ya kasance hanya wacce mutane da yawa suke samu kuɗi masu tarin yawa koda kuwa suna kwance suna bacci a gida. 

NB: bawai daga kayi applying bane zasuyi approving su fara baka talla yina daukar lokaci kafin su gama review.

Post a Comment

Previous Post Next Post