Trending

Adadin Yadda Ya kamata ka Motsa Jikinka duk sati (WHO)

Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar da adadin motsa jikin da ya kamata ka yi duk sati.Hukumar Lafiyar ta Duniya, wato World Health Organization (WHO), ta bayar da shawara kan nau’i da kuma adadin motsa jikin da manya ya kamata su riƙa yi domin samun kuzari, inganta garkuwar jiki, bunƙasa karsashin jiki da kuma walwala:

— yi matsakaicin motsa jiki, kamar ayyukan gida, tafiya, na aƙalla mintina 150 – 300 duk sati; ko kuma

— yi matsanancin motsa jiki, kamar gudu, tuƙa keke, wasan ƙwallon ƙafa, na aƙalla mintina 75 – 150 duk sati.

Bugu da ƙari, Hukumar Lafiya ta Duniyar ta fitar da shawara cewa: yara da waɗanda ke cikin shekarun balaga (shekara 10 — 19) su riƙa motsa jiki na aƙalla mintina 60 kowace rana.

Neman shawara ko tattaunawa da likitan fisiyo kafin fara duk wani atisaye ko motsa jiki zai ceto ka daga matsalolin da ke biyo bayan farawa da ka kamar raunuka ko bugun zuciya musamman ga masu fama da cutuka kamar ciwon zuciya, hawan jini, ciwon siga ko asma.

Physiotherapy

Spread to

Related Articles

Back to top button